Lahadi 10 Mayu 2026 - 21:29
Silsilar Tattaunawa Kan Mahdawiyya (27) | Raj’ar Annabawa, Imamai da Muminai 

Hauza/ Annabawa, Imamai ma’asumai (AS) da kuma muminai masu tsarki — bisa ga riwayoyi— za su dawo duniya a lokacin raj’a.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, ana gabatar da jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yada koyarwa da ma’arifa da suka shafi Imamuz Zaman (AJ) ga ku masu daraja.

Bisa ga ruwayoyi, Annabawa, Imamai ma’asumai (AS) da muminai suna daga cikin waɗanda za su dawo wannan duniya a lokacin raj’a.

Ana iya rarraba waɗannan ruwayoyi zuwa rukuni huɗu:

A) Ruwayoyin da suka yi magana gaba ɗaya game da dawowar Annabawa da Imamai (AS):

Imam Ja'afar Sadiƙ (AS) a cikin tafsirin ayar nan:

«إِنَّا لَنَنصُرُ رُسُلَنَا وَالَّذِینَ آمَنُوا فِی الْحَیاةِ الدُّنْیا وَیَوْمَ یَقُومُ الْأَشْهَادُ؛  

"Lalle ne za Mu taimaki manzanninMu da waɗanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da masu shaida za su tashi.» (Suratul Ghafir: 51)

ya ce:

«ذلک والله فی الرجعة، أما علمت أن أنبیاء کثیرة لم ینصروا فی الدنیا وقتلوا والائمة بعدهم قتلوا ولم ینصروا، ذلک فی الرجعة.»  

"Na rantse da Allah cewa wannan ayar za ta tabbata ne a lokacin raj’a. Shin ba ku sani ba cewa Annabawa da yawa ba a taimaka musu a duniya ba kuma an kashe su, haka ma Imamai bayan su an kashe su kuma ba a taimaka musu ba? Wannan taimako da nasara za su tabbata ne a lokacin raj’a." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 5, sh. 384)

B) Ruwayoyin da suka ambaci 'adadi' game da raj’ar Annabawa:

Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«ویقبل الحسین فی أصحابه الذین قتلوا معه ومعه، سبعون نبیا، کما بعثوا مع موسی بن عمران.»  

"Lokacin da Imam Hussain (AS) zai dawo tare da sahabbansa waɗanda aka kashe tare da shi, Annabawa saba’inbma za su dawo tare da shi, kamar yadda aka aiko saba’in tare da Musa ɗan Imran (AS)." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 4, sh. 89)

C) Ruwayoyin da suka ambaci raj’ar wasu Annabawa da Imamai da sunayensu:

Imam Muhammad Baƙir (AS) ya ce:

«وَ إِنَّ دَانِیَالَ وَ یُوشَعَ یَخْرُجَانِ إِلَی أَمِیرِ اَلْمُؤْمِنِینَ یَقُولاَنِ صَدَقَ اَللَّهُ وَ رَسُولُهُ.»  

"Hakika Daniyal da Yusha’u (AS) za su dawo duniya a lokacin raj’ar Amirul Muminin (Ali (AS), kuma za su ce: "Allah da Manzonsa sun yi gaskiya." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 62)

Haka kuma Imam Zainul Abidin (AS) ya ce:

«یرجع إلیکم نبیکم صلی الله علیه وآله وأمیرالمؤمنین علیه‌السلام والائمة علیهم‌السلام.»  

"Annabinku (SAWA) da Amirul Muminin (Ali (AS) da Imamai (AS) za su sake dawowa gare ku." (Mu‘ujamu Ahadith al‑Imam al‑Mahdi, j. 5, sh. 327)

Haka kuma Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«أَوَّلُ مَنْ یَرْجِعُ إِلَی اَلدُّنْیَا اَلْحُسَیْنُ بْنُ عَلِیٍّ عَلَیْهِ السَّلاَمُ.»  

"Na farkon wanda zai dawo duniya shi ne Hussain ɗan Ali (AS)." (Bihar al‑Anwar, j. 53, sh. 46)

D) Ruwayoyin da suka ba da labarin raj’ar mutanen kirki daga al’ummomin da suka gabata da kuma al’ummar Musulunci:

Imam Ja’afar Sadiƙ (AS) ya ce:

«یَخْرُجُ اَلْقَائِمُ مِنْ ظَهْرِ اَلْکَعْبَةِ مَعَ سَبْعَةٍ وَ عِشْرِینَ رَجُلاً خَمْسَةَ عَشَرَ مِنْ قَوْمِ مُوسَی عَلَیْهِ السَّلاَمُ اَلَّذِینَ کَانُوا یَهْدُونَ بِالْحَقِّ وَ بِهِ یَعْدِلُونَ وَ سَبْعَةٌ مِنْ أَهْلِ اَلْکَهْفِ وَ یُوشَعُ بْنُ نُونٍ وَ سَلْمَانُ وَ أَبُو دُجَانَةَ اَلْأَنْصَارِیُّ وَ اَلْمِقْدَادُ وَ مَالِکٌ اَلْأَشْتَرُ فَیَکُونُونَ بَیْنَ یَدَیْهِ أَنْصَاراً أَوْ حُکَّاماً.»  

"Qa’im (Imam Mahdi AS) zai bayyana daga bayan Ka’aba tare da mutum ashirin da bakwai, goma sha biyar daga mutanen Musa (AS) waɗanda suka kasance suna shiryarwa da gaskiya kuma suna yin adalci da ita, da kuma mutum bakwai daga Ashabul Kahf, Yusha’u ɗan Nun, Salman, Abu Dujana al‑Ansari, Miƙdad da kuma Malikul Ashtar;  kuma za su kasance a gabansa a matsayin mataimaka ko shugabannin rundunarsa." (Rawdat al‑Wa’izin, j. 2, sh. 266)

Wannan tattaunawa za ta ci gaba...

An ɗauko daga littafin "Negine Afarinesh”, tare da ɗan gyara kaɗan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha